Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Fitar Da Naira Biliyan 250 Domin Bai Wa Manoma Rance

[ad_1]

A ci gaba da kokarin da ta ke yi, gwamnatin tarayya ta fitar da kimanin naira biliyan 250, domin bai wa manoman kasar nan rancen kudi domin yin noma.

Kazalika, gwamnatin ta kuma fitar da kimanin buhunhunan Takin Zamani miliyan 2.15, da nufin tallafa wa manoman kasar, musamman domin a kara bunkasa samar da wadataccen abinci.

  • Hukumar NPA Ta Karrama Jajirtattun Matan Da Ke Aiki A Hukumar
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kaucewa Takara Mai Hadari

Karamin Minista a ma’aikatar bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Business Daily.

Ministan ya bayyana cewa, wannan daukin na daga cikin matakan da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da dauka, musamman domin magance matsalar samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kalubalen da fannin aikin noma a kasar ke fuskanta.

“Wadannan tsare-tsaren da gwamnatin ta samar da su, na ci gaba da tafiya, yadda ya dace, sannan kuma gwamnatin ta fara wanzar da daukar matakan gaggawa kan samar da wadataccen abinci a kasar ne, tun bayan da shugaban kasa a shekarar 2023, ya ayyana dokar ta baci, a fannin na aikin noma na kasar nan,” a cewarsa.

“Mun tafi ne kai tsaye, a kan shirye-shiyen da muke yi tare da yakinin cewa, za su taimaka matuka wajen kara bunkasa fannin aikin noma a kasar ciki har da noman rani,”in ji ministan.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta kuma rungumi tsarin ganin ana yin noma a kasar har zuwa na tsawon shekara daya, musamman da nufin kara samar da wadataccen abinci a kasar nan.

“A wajen yanzu, batun yin noma a kasar ya wuce kawai yin noma a lokacin damina ko kuma a lokacin rani, amma tsarin a yanzu shi ne, yin noman har na tsawon shekara daya” in ji Abdullahi.

Har ila yau, ya yi nuni da cewa; batun samar da wadataccen abinci a kasar, ya wuce maganar yin noman shi kan shi, amma batu ne da ke nufin samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar.

Kazalika, ministan ya yi nuni da cewa; duk da damuwar karin farashin kayan abinci a daukacin kasuwanin kasar, amma har yanzu ana ci gaba da samun wadataccen abinci a kasar.

“Duk kasuwar da ka shiga a daukacin fadin kasar nan, zai yi wuya ka ga babu kayan abincin da ake sayarwa, akwai wadaccen abinci sai dai kawai a ce babu kudin saya, wannan shi ne kwai babban kalubalen, amma duk da haka, gwamnatin ba ta yi kasa a guiwa ba, domin kuwa ta mayar da hankali wajen rage farashin wasu amfanin gona, domin ‘yan kasar su saya a farashi mai rahusa,” in ji Ministan. “Mun gano amfanin gonar da muka san cewa; ‘yan kasar nan sun fi yin amfani da shi a daukacin fadin kasar, musamman Rogo wanda aka fi yawan amfani da shi a fadin kasar, sai kuma Shinkafa da Masara da Alkama’” a cewar ministan.

Ya kara da cewa, kayan lambu kamar irin su Tumatir da Tattasai da Albasa, an sanya su a cikin jerin kayan da ake samun hauhawar farashinsu, saboda bukatarsu da ake da ita ta yau da kullum.

Abdullahi ya sanar da cewa, ma’aikatar a kwanakin baya, ta samar wa manoman Tumatir dauki, musamman manoman da suke a Jihar Kano, wadanda cutar Tuta absoluta ta lalata gonakinsu na Tumatir.

Kan batun shigo da kayan abinci cikin kasar, ministan ya bayyana cewa; ta dauki wannan matakin na wucin gadi ne, domin daidaita farashin kayan abinci a kasar.

“Misali, bukatar da ake da ita a kasar ta Masara, ta kai ta kimanin tan miliyan 25.

Ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya a karkashin shirin aikin noma na babban bankin Nijeriya (CBN), ta amince da a fitar da buhunhunan Takin Zamni kimanin miliyan 2.15, musamman domin a rage tsadar aikin noma a tsakanin manoman kasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *