Raphinha Zai Shafe Makonni 5 Yana Jinyar Raunin Da Ya Samu A Wasannin Ƙasa Da Ƙasa
[ad_1]
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta rasa babban ɗan wasanta Raphinha na tsawon mako biyar sakamakon zaman jinyar raunin da ya samu a wasan da ƙasarsa ta Brazil ta yi rashin nasara a hannun Faransa da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka buga a ranar Alhamis, daga cikin wasannin da zai rasa akwai wasan kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai da Atletico Madrid a watan Afrilu.
Raphinha ya ji rauni ne a lokacin da Brazil ta sha kashi a hannun Faransa da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka buga da Faransa a Amurka ranar Alhamis, a cikin wata sanarwa, hukumar ƙwallon ƙafa ta Brazil ta ce Raphinha da ɗan wasan baya na Roma Wesley duk sun samu rauni a wasan na ranar Alhamis da sukayi da ƙasar Faransa.
- Kasar Sin Ta Yi Tir Da Hare-haren Amurka Da Isra’ila Kan Wata Makaranta A Iran
- An Damfari Masu Amfani Da Wayar Hannu Naira Biliyan 12.5 A Shekara 4
A nata ɓangaren Barcelona ta fitar da sanarwar cewa tsohon ɗan wasan na Leeds United zai shafe tsawon mako 5 yana Jinyar raunin, “An kiyasta cewa Raphinha zai shafe tsawon makonni biyar,” in ji Barcelona, Raphinha muhimmin ɗan wasa ne ga ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta yankin Catalonia, ba zai buga wasanni biyu na kusa da na kusa da na ƙarshe da Barcelona za ta haɗu da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid a watan Afirilu.
Ɗan wasan mai shekaru 29, wanda ya zura wa Barcelona ƙwallaye 19 a wannan kakar wasan ta bana, zai kuma rasa wasannin gasar La Liga da suka haɗa da Atletico Madrid, Espanyol, Celta Vigo da Getafe.
Barca na fatan Raphinha ya murmure kafin buga wasan El Clasico da Real Madrid a ranar 10 ga watan Mayu, ko kuma wasan kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai da Arsenal ko Sporting Lisbon a ranar 29 ga watan Afrilu.
[ad_2]
Source link