Cinikayyar Waje Ta Jihar Xinjiang Ta Bunkasa A Shekarar 2025

[ad_1]

Mataimakin daraktan sashen cinikayya na gwamnatin jihar Xinjiang ta arewa maso yammacin kasar Sin, Li Xuan, ya ce cinikayyar waje ta jihar Xinjiang ta bunkasa sosai a shekarar 2025 da ta gabata. Li Xuan ya ce bunkasar cinikayyar waje ta jihar ta karu da kaso 19.9 bisa dari a mizanin shekara-shekara.

Wasu alkaluma da ofishin watsa labarai na gwamnatin jihar ta Xinjiang ya fitar, sun nuna yadda jihar ta zamo ta daya tsakanin biranen kasar Sin da suka kai matsayin larduna a fannin saurin bunkasar cinikayyar waje.

Da yake tsokaci kan sassan ci gaban da jihar Xinjiang ta samu a wannan fanni, a yayin taron manema labarai na jiya Laraba, Li Xuan ya ce jihar ta gudanar da hada-hadar shige da ficen hajoji a shekarar 2025 da suka kai darajar Yuan biliyan 520.37, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 74.6.

Jami’in ya kara da cewa, jihar Xinjiang ta kaddamar da tsarin kara bude kofa mai matakai da dama, da dandali mai sassa uku, karkashin jagorancin yankin gwaji da gudanar da cinikayya cikin ’yanci, da tallafin yankunan raya tattalin arziki da fasahohin samar da ci gaba na kasa, da yankunan kan iyakoki na hadin gwiwar raya tattalin arziki, da cikakkun yankunan hada-hada na musamman.

Cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da rabin daukacin jiragen kasa na dakon hajoji tsakanin Sin da Turai sun bar kasar Sin ne ta jihar Xinjiang, kuma manyan tashoshin yankin sun cimma nasarar samar da hidimomin kwastam na samar da izinin shige da fice na ko da yaushe. Yayin da a yanzu haka, filin jirgin sama na Urumqi Tianshan ke karbar jirage masu sufurin hajoji kan hanyoyin kasa da kasa 37, wadanda suka hade birane 36 na kasashe da yankunan duniya 22. Kazalika, a shekarar 2025, ikon filin jirgin na karbar hajoji ya karu da kaso 152.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *