An yi wa wata mai shekara 70 fyaɗe a Kaduna
[ad_1]
Wata babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a garin Kafanchan ta bayar da umarnin tsare wani manomi mai suna Timothy Ayock a gidan gyaran hali bisa zargin yi wa wata bazawara fyaɗe.
Ayock dai na fuskantar shari’a kan laifuka biyu da suka haɗa da: fyaɗe da aikata laifuka, saɓanin sashe na 257 da 237 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Kaduna na shekarar 2017.
Lauyan jihar daga Ma’aikatar Shari’a, Daniel Isah ya shaida wa kotun cewa, wanda ake ƙara ya yi lalata da wata bazawara mai shekara 70 da ƙarfi a unguwar Tagama da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a ranar 26 ga Disamba, 2025.
Lokacin da ake tuhumarsa da aikata laifin, ya musanta laifin.
Daga nan sai mai gabatar da ƙara ya roƙi kotun da ta ɗage sauraron ƙarar don bai wa jihar damar tabbatar da ƙarar da ta shigar a kan wanda ake ƙara.
Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun, Michael Eugene, ya bayar da umarnin a tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Kafanchan.
Eugene ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har sai ranar 5 ga watan Maris, 2026 kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link