Amurka_Isra’ila Akan Iran: Rikicin Gabas ta Tsakiya Ya Fara Daukar Sabon Salo
[ad_1]
Tun bayan barkewar zanga-zangar tsadar rayuwa da ta rikide ta koma tarzomar kin jinin gwamnati daga wasu acikin al’ummar Iran a karshen Disamba 2025 da farkon Janairu 2026, an samu karuwar muhawara tsakanin Iran da Amurka, ciki har da tsauraran kalamai da barazanar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu.
Amurka ta nuna goyon baya ga masu zanga-zangar ta Iran, tana kira ga gwamnatin Tehran da ta daina yin amfani da karfi wajen murkushe su, wanda hakan ya sanya Shugaba Donald Trump ya yi barazanar cewa, Washington na iya “taya” masu zanga-zangar ko ma daukar matakai idan hukumomin Iran suka yi amfani da karfi wajen kashe mutane.
- ASUU Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana Hudu Kan Sabon Tsarin Albashi
- UBEC Ta Kaddamar Da Tsarin Dala Miliyan 552 Domin Ilimin Bai-daya
A nata martanin, Iran ta zargi Amurka da tsoma baki sosai a harkokinta na cikin gida, tana cewa wannan wani yunkuri ne na kifar da gwamnatinta, wanda kuma ba za ta lamunci hakan ba. A cikin martanin da aka fitar a hukumance, Tehran ta yi gargadin cewa, duk wani yunkurin Washington na kai hari Tehran zai dagula zaman lafiyar yankin, inda ta sha alwashin mayar da martanin hari kan duk wani sansanin sojin Amurka dake yankin da kuma duk kasar da ta bari Amurka ta yi amfani da kasarta ko sararin samaniyarta wurin kai mata (Iran) hari.
Amma Amurka ta yi biris da duk wannan martanin, inda a ranar 28 ga watan Fabrairu, ta hada kai da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare cikin Iran wanda hakan ya yi sanadin mutuwar Babban jagoran addini na kasar, Ayatullah Alkamnei tare da wasu kwamandojin sojojin juyin juya hali (IRGC) na Iran.
Rahotanni na nuna cewa, bayan wata guda da fara hare-haren hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, yankin Gabas ta Tsakiya na kara fadawa cikin rikici mai tsanani, inda yawan mace-macen fararen hula ke karuwa, yayin da rikicin ke kara yaduwa zuwa wasu sassa na yankin.
Bincike ya nuna cewa, wannan rikici bai zama dole ba, domin akwai hanyoyin diflomasiyya da za a iya bi kafin fara hare-haren amma aka yi watsi da su, sabida rashin girmama tsarin doka na Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ya kara dagula al’amura maimakon kawo mafita.
Masana harkokin kasa da kasa sun bayyana damuwa kan yadda aka kaddamar da wannan hare-haren na son rai, musamman dangane da rashin samun amincewar Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya kafin daukar matakin soja, wanda hakan na iya kawo cikas ga dokokin kasa da kasa da kuma rage darajar tsarin doka a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa, maimakon samun kwanciyar hankali da Amurka ta yi ikirarin samarwa, hare-harenta sun kara jefa yankin cikin wani hali mawuyaci. Tarihi ya nuna cewa, irin wadannan matakan hare-hare na Amurka, ba sa haifar da komai sai dai haddasa rashin zaman lafiya mai dorewa, kamar yadda aka gani a sauran kasashen da irin hakan ta faru da su, kamar Libya, Iraq, Afghanistan da Syria.
Masana sun jaddada cewa, hanyar soja kadai ba za ta iya kawo cikakken tsaro ba. Sun ce yankin na bukatar zaman lafiya, ci gaba da tattaunawa, da kuma hanyoyin siyasa domin warware matsalolin da ke akwai.
Sam bai dace ba, manyan kasashe su rika take kanana, kamar ana rayuwar dabbobin daji. Ya dace, kasashen duniya su guji daukar matakai na kashin kai, su kuma mutunta dokokin kasa da kasa domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a duniya.
[ad_2]
Source link