An yi jana’izar mutanen da Lakurawa suka kashe a Masallaci a Kebbi

[ad_1]



An yi jana’izar maza biyar da mace ɗaya da ’yan Ta’addan Lakurawa suka kashe a wani Masallaci da ke garin Dadinkowa, a Ƙaramar Hukumar Maiyama a Jihar Kebbi.

Babban limamin garin ne ya jagoranci sallar jana’izar da safiyar ranar Alhamis, inda al’ummar yankin suka halarci jana’izar ciki da jimami.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a daren ranar Laraba yayin da jama’a ke sallar Asham.

Take sukka kashe mutum biyar a cikin masallacin.

Mace guda da aka harba a wajen Masallacin kuma ta rasu daga baya a asibiti sakamakon raunukan da ta samu.

Bayan faruwar harin, jami’an tsaro sun isa yankin domin tabbatar da tsaro da kwantar da hankalin jama’ar garin.

Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba, yayin da al’umma ke zaman ɗar-ɗar.

Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana:


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *