Masallacin Al-Ahfad ya shirya buɗe baki tare da kiristoci a Gombe

[ad_1]



Masallacin Al-Ahfad da ke unguwar Nasarawo a cikin birnin Gombe ya shirya buɗa baki na watan Ramadan tare da limaman Musulmi da na Kirista, a wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai.

Babban Limamin masallacin, Dakta Umar Dokaji ya bayyana cewa, an tsara taron ne domin inganta fahimtar juna da danƙon zumunci tsakanin Musulmi da Kiristoci, musamman a daidai lokacin da ɓangarorin biyu ke gudanar da azumin su na addini.

A cewarsa, haɗuwar ta nuna muhimmancin zaman tare cikin lumana, tare da zama abin koyi ga sauran al’ummomi a faɗin ƙasar nan.

Ya ce, Najeriya na fuskantar ƙalubale da suka shafi rashin jituwa na addini da ƙabilanci, don haka akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen samar da dandalin tattaunawa da zai hana ɓarkewar rikice-rikice.

“Wannan shiri ya zo ne a lokacin da ake fuskantar kalubale da dama a ƙasar nan, ciki har da zarge-zargen tsangwamar addini da tashe-tashen hankula a wasu yankuna,” in ji Dokta Dokaji.

“Na yi imani cewa, irin waɗannan taruka za su ƙara haɗa kan al’umma tare da rage yiwuwar samun rikice-rikicen addini.”

Limamin ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya, tare da jaddada muhimmancin tallafa wa marasa ƙarfi a cikin al’umma.

Ya ce, adalci shi ne ginshiƙin samar da dawwamammen zaman lafiya a ƙasar.

A nasu ɓangaren, limaman Kirista da suka halarci buɗa bakin sun nuna jin daɗinsu da godiya ga masallacin kan wannan kyakkyawan mataki, suna mai cewa, hakan wata alama ce ta haƙuri da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai a Gombe.

Da yake magana a madadin baƙin Kiristocin, Rabaren Abare Kalla ya ce taron zai ƙara ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci mazauna unguwar Nasarawo.

Ya kuma tuna da yadda a baya al’ummomin biyu suka warware wani saɓani kan wurin ibada cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, yana mai cewa wannan abin alfahari ne da ke nuna ƙarfin haɗin kai da tattaunawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *