Sin Ta Yi Kira Da A Koma Teburin Tattaunawa Game Da Batun Nukiliyar Iran
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin na kira da a gaggauta dakatar da aiwatar da matakan soji, tare da komawa tattaunawa da gudanar da shawarwari, kan batun nukiliyar kasar Iran.
Mao Ning ta bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, biyo bayan sanarwar shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA a jiya Litinin, dake cewa ba wasu shaidu na hakika da suka tabbatar cewa Iran tana da cikakken shirin kera makaman nukiliya.
Jami’ar ta ce har kullum kasar Sin na kira da a warware batun nukiliyar Iran ta hanyar lumana, ta amfani da shawarwari da hawa teburin sulhu, kana a martaba halastattun hakkokinta na amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana.
Mao ta kara da cewa, kasar Sin ta lura da yadda Iran ta sha nanata cewa, ba ta da wata aniya ta samar da makaman kare dangi, ta kuma himmatu wajen hawa teburin shawarwari da Amurka a baya-bayan nan, don haka ya wajaba a mayar da warware batun nukiliyar Iran din kan turbar diflomasiyya. Daga nan sai ta jaddada kiran da kasar Sin ke yi ga dukkanin sassa, da su martaba manufar kasa da kasa ta dakile bazuwar makaman kare dangi, da kare zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link