Harin Iran: Amurka da Isra’ila sun saɓa wa dokokin duniya — Macron

[ad_1]



Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce babu tantama Amurka da Isra’ila sun saɓa wa dokokin duniya wajen ƙaddamar da hari kan ƙasar Iran, abin da ya haifar da yaƙin da ke gudana yanzu haka wanda ba su amince da shi ba.

Sai dai shugaban ya kuma zargi Iran da alhakin haifar da wannan matsalar dangane da abinda ya shafi shirin nukilyarta da goyan bayan ayyukan ta’addanci a yankin, tare da harbe jama’ar ƙasar da ke zanga zanga a watan Janairu.

RFI ya ruwaito Macron yana sanar da cewar Faransa ta tura katafaren jirgin ruwan da ke ɗaukar jiragen yaƙi Gabas ta Tsakiya domin tabbatar da tsaro a yankin, sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran.

A jawabin da ya yi wa al’ummmar ƙasar a Talatar nan, Macron ya ce sun yanke hukuncin ɗaukar matakin ne na tura ‘Charles de Gaulle’ mai ɗauke da jiragen yaƙi na Rafael Jet saboda abin da ke faruwa a yankin.

Macron ya ce sakamakon yarjejeniyar tsaron da suke da ita tsakanin Faransa da Kuwait da Bahrain da kuma Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa, sun tura na’urorin kakkaɓo makamai domin kare su daga makaman da Iran ke harba musu.

Shugaban ya ce daga cikin makaman da za su tura yankiin harda wanda za a kai Cyprus, ƙasar da ke ci gaba da fuskantar barazana daga Iran.

Macron ya tabbatar da cewar Faransa ta kakkaɓo wasu daga cikin makamai masu linzamin da Iran ta harba, ba tare da ƙarin bayani a kai ba.

Shugaban ya kuma nuna rashin amincewarsa da shirin Isra’ila na tura sojoji cikin ƙasar Lebanon, abin da ya kira a matsayin babbar takala mai tattare da kura-kurai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *