’Yan Najeriya masu aikin jinya a Birtaniya sun haura 16,000
[ad_1]
Aƙalla ma’aikatan jinya da na unguwar zoma ’yan asalin Najeriya 16,156 ne suka yi hijira kuma yanzu haka suke aiki a kasar Birtaniya daga shekarar 2017 zuwa 2025.
Wannan adadi ya fito ne daga sabbin bayanan da aka samu daga rajistar Hukumar da ke kula da ayyukan ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta (NMC), kamar yadda jaridar Punch ta samo.
Alkaluman sun nuna yadda ake samun hijirar ma’aikatan kiwon lafiya da aka horar a Najeriya, inda ƙwararru ke barin ƙasar domin zuwa inda aka fi samun albashi mai tsoka, ci gaban aiki da kuma ingantattun yanayin aiki.
Hijirar ma’aikatan na lafiya na haifar da babbar matsala ga tsarin kiwon lafiya na Najeriya, musamman a yankunan da ba a kula da su sosai, inda hakan ke nuna buƙatar gaggawa wajen riƙe ma’aikatan da kuma ƙarfafa ƙasa wajen samar da ƙwararrun ma’aikatan.
NMC ita ce hukumar da ke da alhakin rajista da binciken ƙwararrun ma’aikatan jinya, masu haihuwa da kuma unguwar zoma a Birtaniya.
A wata tattaunawa ta imel ga wakilin jaridar, NMC ta ce: “Ya zuwa ranar 30 ga watan Satumba, 2025, akwai ma’aikatan jinya 16,156 a rajistar ma’aikatan Burtaniya wadanda suka yi karatu a Najeriya.”
Rahoton da aka fitar a watan Maris ya nuna cewa Najeriya ta kasance ta uku a jerin ƙasashen da suka fi samar da ma’aikatan jinya da aka horar a kasashen waje a Birtaniya, bayan kasashen Philippines da India.
Haka kuma rahoton ya nuna raguwar ɗaukar ma’aikata daga ƙasashen waje, ciki har da ƙasashen uku na farko: India, Philippines da Najeriya.
Rahoton ya ƙara da cewa duk da ƙaruwa a yawan ƙwararrun da aka horar a Birtaniya da ke shiga rajistar NMC, saurin bai isa ya cike gibin da raguwar ɗaukar ma’aikata daga waje ya haifar ba.
Saboda haka, girman rajistar gaba ɗaya ya ragu a shekarar da ta gabata.
Bugu da ƙari, rahoton kididdigar lafiya na Najeriya na 2025 da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta fitar a watan Nuwamba ya nuna cewa jimillar likitoci, ma’aikatan jinya, masana kimiyyar harhada magunguna da kwararrun masu gwaje-gwaje 43,221 sun bar ƙasar zuwa kasashen waje daga tsakanin 2023 zuwa 2024.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link