Fafaroma ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kare rayukan ’yan Najeriya

[ad_1]



Fafaroma Leo na XIV ya bayyana baƙin cikinsa kan kisan gillar da aka yi a wasu al’umma a Najeriya, inda ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan kare rayukan ’yan ƙasarta.

Aƙalla mutum 100 ne aka kashe a ƙauyen Woro da wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

Shugabannin yankin sun ce an binne mut 75 a ranar Laraba, yayin da aka binne wasu 13 a ranar Alhamis.

Har yanzu akwai wasu mutane da ba a san inda suka shiga ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Fafaromannya ce ya samu labarin hare-haren waɗanda suka yi matuƙar baƙanta masa rai.

“Cikin baƙin ciki da damuwa na samu labarin hare-haren da aka kai wa al’ummomi daban-daban a Najeriya, wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dama.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga dukkanin waɗanda ta’addancin ya shafa.”

Fafaroman ya buƙaci hukumomin Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen kare rayukan jama’a da tabbatar da tsaron kowane ɗan ƙasa.

Wannan martani ya biyo bayan na Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda shi ma ya yi Allah-wadai da hare-haren tare da bayyana cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na tare da Najeriya a yaƙi da ta’addanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *