Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba.
Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da su a Kudanci da Arewa maso Gabashin ƙasar.
Jaridar Vanguard ta bayyana cewa matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.
Sai dai EU ta ce akwai abubuwa da dama da ke haifar da rikicin ba addini kaɗai ba ciki har da talauci da siyasa.
“Mun fahimci cewa akwai abubuwa masu yawa da ke haifar da rikici a Najeriya, addini guda ne daga cikinsu, amma ba shi kaɗai ba,” in ji Mista El Anouni.
ECOWAS ta yi watsi da iƙirarin Trump
Ita ma Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ta yi watsi da abin da ta kira iƙirarin ƙarya mai cike da hatsari da shugaban Amurka ya yi cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na far wa kiristoci tare da kashe su a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata, ECOWAS ta ce irin wannan barazana ta Shugaba Trump ka iya ta’azzara matsalar tsaro tare da haifar da matsalar zamantakewa a yankin da dama ke fama da matsalar masu tsattsauran ra’ayi.
ECOWAS ta jaddada cewa hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a yankin Afirka ta Yamma na shafar mutanen da ba su ji ba su gani ba, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ko jinsi ba.
Dangane da hakan ne ƙungiyar ta buƙaci ƙasashen duniya su tallafa wa kowace ƙasa wajen yaƙi da ta’addanci da ke shafar kowa da kowa.