Sakkwata sun yi zanga-zanga kan kashe mutane 5 da sace Hakimi da limamai
[ad_1]
’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu.
Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja.
A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu.
“Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace mana mutane kuma babu wasu jami’an tsaro da aka kawo mana don kare mu.”
Ya ce ’yan bindigar sun tashi ƙauyuka uku a ranar Juma’a, sun tafi na biyu dana uku a ranar Assabar da Lahadi.
“A garin Rinaye sun sace mai garinmu da duka limaman garin bayan sun kashe mutum uku sun yi garkuwa da wasu mutanen garin da ba a tantance yawansu ba, a wannan Asabar da Lahadi.
“Shekaranjiya sun shiga garin Aske dodo da Tungar Barkenda Jandutse duk waɗannan wurare babu mutane a cikinsu yanzu, sun kashe mutane biyu da yin garkuwa da wasu 15,” a cewar majiyar.
Ya ce hukumomin tsaro da gwamnati ba a abin da suka yi a yanzu, ko jaje ba a kai musu ba.
Malama Tunba mai yara biyar mata uku da maza biyu daga ƙauyen Jandutse ta ce yanzu haka ba ta san inda ’ya’yanta suke ba tun da suka gudu a ranar Assabar, a haka ta yini ba abin da ta sa a bakinta.
Tumba ta yi kira ga gwamnati ta taimaka musu da tsaro mu zauna a gidajensu cikin rufin asiri, wahalar da suke ciki ta yi yawa.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta jiha SEMA sun ce sun san da zaman ’yan gudun hijirar da suka gudu kan matsalar ’yan bindiga.
Bayanin ya ce, “A Ƙaramar hukumar Shagari ɗaruruwan mutane sun bar muhallansu kan rashin tsaron da ya kunno kai a yankin suna neman ɗauki.
“Don ganin halin da ake ciki, hukumomin sun tafi rukunin gidaje 30 a ƙaramar hukumar inda mutanen suka zauna sun tuntubi hakiman mutanen daga cikinsu akwai Hakimin ‘Yan Dundaji, Malam Muhammad Bello Magaji, da Maigarin Tungar-Barke, Muhammadu Tudu, wanda ya tabbatar da harin da aka kai musu kwana uku baya, yana da ’yan gudun hijira da yawa.
Sauran ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Tungar-Barke, Lungu, Aske-Dodo, Tungar-Doruwa, Zango, ‘Yan Yandu, Tungar Na’anza, Ila, da sauransu.
A halin da ake ciki hukumomin na kira ga gwammati ta kawo ɗaukin gaggawa musamman samar da tsaro a ƙauyukan don mutanen su koma gidajensu cikin aminci.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban karamar hukumar Shagari Honarabul Alhaji Maidawa sai dai bai samu jin ta bakinsa ba har zuwa haɗa labarin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link