Mahaifiyar El-Rufai Ta Rasu, Akwai Yiwuwar Ba Zai Halarci Jana’izarta Ba
[ad_1]
Hajiya Umma El-Rufai, Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta rasu.
Ɗansa, Bello El-Rufai ne, ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a ta shafinsa na Facebook, inda ya ce kakarsa ta rasu sa’o’i da suka gabata, tare da roƙon a yi mata addu’a.
- Gayyato Jakadun Kasashen Waje 17 Ya Kara Wa Bukukuwan Sallah Armashi A Katsina
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
Ya gode wa Allah kan irin rayuwar da ta yi, sannan ya roƙi Allah Ya jikanta da rahama.
Rasuwar na zuwa ne a daidai lokacin da El-Rufai ke tsare inda ake tuhumarsa da laifiuka da dama, lamarin da ya sa ake hasashen ba lallai ya halarci jana’izarta ba.
Har yanzu ba a bayyana shirye-shiryen jana’izar ba.
[ad_2]
Source link