Sojoji sun kama kayayyakin da za a kai wa ’yan ta’adda a Borno
[ad_1]
Dakarun Sojin Ƙasan Najeriya sun tare wasu kayayyaki da ake zargin za a kai wa ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Jihar Borno.
Aikin ya gudana ne a ranar Juma’a a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama, kwanaki kaɗan bayan kama irin waɗannan kayayyaki a jihar.
Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce sojojin sun kuma gano tare da tarwatsa wani bam da aka dasa a kan hanyar Damboa zuwa Komala.
Ya bayyana cewa a ranar 17 ga watan Disamba, 2025, sojojin rundunar yayin sintiri a kan babbar hanyar Damboa zuwa Komala, sun gano wani bam da aka dasa.
Sojojin sun ɗauke bam ɗin cikin tsaro sannan suka tarwatsa shi, lamarin da dawo da zaman lafiya da damar zirga-zirga a yankin.
A wani aikin kuma da aka gudanar a ranar 19 ga watan Disamba, 2025, sojojin da ke bincike a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama sun tare wata mota mai lambar Legas, AKD 244 YE.
Motar na ɗauke da kayan abinci da lemun ƙara kuzari da ake zargin an shirya kai wa ’yan Boko Haram da ISWAP da ke unguwar Kirawa a Ƙaramar Hukumar Gwoza.
An kama mutane biyu bisa zargin hannu a lamarin.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da kayan abinci, lemun ƙara kuzari, wayoyin salula guda uku, katin shaida, zobe, da kuɗi.
An miƙa waɗanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka ƙwato ga sashen leƙen asirin sojoji domin ci gaba da bincike.
Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba daƙile ’yan ta’adda daga samun kayayyakin tallafi, taƙaita zirga-zirgarsu, tare da tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link