Kirsimeti: Sibil Difens ta tura jami’ai 786 don tabbatar da tsaro a Gombe

[ad_1]



Hukumar Sibil Difens a Jihar Gombe, ta tura dakarunta 786 domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a faɗin jihar.

Kwamandan hukumar a Jihar Gombe, Kwamanda Jibrin Idris ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar.

Sanarwar ta ce wannan shiri zai fara aiki ne daga 25 ga watan Disamba, 2025 zuwa 1 ga watan Janairu, 2026, da nufin kare rayuka, dukiyoyi a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Kwamanda Idris, ya umarci Kwamandojin Yankuna, Shugabannin Sassa da Kwamandojin Rukuni-rukuni da su tabbatar da tsaro wuraren ibada, wuraren taron jama’a da sauran muhimman wurare a faɗin jihar.

Ya ce an kuma bai wa jami’an umarnin kare kayayyakin gwamnati da masu zaman kansu, su tabbatar da doka da oda yayin da kuma bayan kammala bukukuwan.

Kwamandan ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin daƙile duk wata barazana da kuma tabbatar da bukukuwan sun gudana cikin kwanciyar hankali.

Yayin da yake miƙa sakon taya murna na Kirsimeti ga Kiristoci a Jihar Gombe, Idris ya buƙaci al’umma da su kasance masu lura, da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi.

“Tsaron masu ibada, mazauna gari da baƙi shi ne babban abin da muka sa a gaba. Muna kira ga jama’a da su taimaka wa hukumomin tsaro ta hanyar bayar da bayanai a kan lokaci,” in ji shi.

Rundunar ta kuma bayar da lambobin kir-ta-kwama domin ɗaukar mataki cikin gaggawa; 08027370023, 08036541695, 08032917970 da 07062885727.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *