Ana Ganin Yanayi Na Tabbas Wajen Tarukan Majalisun Kasar Sin
[ad_1]
Bisa wani rahoton da aka gabatar da shi wajen dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya, an ce yanayin rashin tabbas daya ne daga cikin manyan abubuwan da suke haifar da barazana ga al’ummun kasashe daban daban a shekarar 2026 da muke ciki. Sai dai a nata bangare, kasar Sin tana samar da cikakken yanayi na tabbas, da ake iya ganin alamarsa wajen tarukan shekara-shekara na majalisun NPC da CPPCC, wato hukumar koli ta kafa dokoki da hukumar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar, dake gudana a birnin Beijing yanzu.
Yanayin tabbas da aka ga alamarsa a tarukan majalisun, da farko dai ya shafi ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci.
A yanzu haka, ’yan majalisun NPC da CPPCC na kasar Sin suna tantance daftarin shirin raya kasar na shekaru 5 masu zuwa, wato tsakanin shekarar 2026 da ta 2030, wanda ya shafi zamanantar da tsarin masana’antu, da inganta kayayyakin more rayuwar jama’a, da raya kimiyya da fasaha, da kirkiro sabbin fasahohi, gami da sauya zuwa salon raya tattalin arziki mai kare muhallin halittu. Wannan shiri ya sa ake hasashen kyakkyawar makomar kasar, musamman ma ta la’akari da kwarewarta ta fuskar aiwatar da shirin da ta tsara, wadda ta tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar ta kaso 5.4% cikin wa’adin shirinta na raya kasa na 2021-2025.
Na biyu kuma, yanayi na tabbas da aka gano wajen tarukan majalisun NPC da CPPCC na kasar Sin ya shafi zumuntar da ke tsakanin Sin da Afirka.
A gefen tarukan majalisun NPC da CPPCC na wannan karo, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kira taron manema labaru don ayyana manufofin kasar a fannin harkar diplomasiyya, inda Fortune Abang, wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Najeriya (NAN), ya yi tambaya kan yanayin huldar dake tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2026. Yayin da ya amsa tambayar, Wang Yi ya nuna kaunar da Sinawa suke da ita ga abokansu ’yan Afirka, inda ya ambaci al’adar ministan wajen kasar Sin ta mai da nahiyar Afirka wurin kaddamar da ziyara ta farko a duk wata sabuwar shekara, da tarihin kasar Sin na ba da tallafi ga kasashen Afirka, da yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ke dora muhimmanci kan raya huldar dake tsakanin bangarorin 2.
Sa’an nan, fanni na 3 da yanayin tabbas da tarukan majalisun NPC da CPPCC suka nuna ya shafa, shi ne yunkurin Sin da Afirka na neman samun ci gaba na bai daya.
Shahararren shehun malami na kasar Najeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana a cikin wata makalar da ya rubuta a kwanan nan cewa, yadda kasar Sin ke aiwatar da shirinta na raya kasa zai haifar da dimbin damammakin raya tattalin arziki ga kasashen Afirka, musamman ma ta la’akari da manufar kasar ta yafe wa kasashe 53 dake nahiyar Afirka harajin kwastam. Ya ce da manufar, gami da niyyar gwamnatin kasar Sin ta sa kaimi ga bangaren sayayya a cikin gidanta, za a ba kasashen Afirka damar fitar da karin kayayyaki, wanda hakan zai taimaka ga bunkasa masana’antu a kasashen Afirka.
Kana a nasa bangare, wani shehun malami dan kasar Kenya mai suna Stephen Ndegwa, ya bayyana cikin wata makalarsa cewa, kasar Sin ta samu nasara a fannin raya harkar samar da kayayyaki masu fasahohin zamani, wadanda ke taimakawa yunkurin kare muhallin halittu a kasashe daban daban. Hakan ya ba kasashen Afirka da ke da wasu ma’adinai masu muhimmanci a fannin masana’antu masu kare muhalli damar shiga a dama da su, a ayyukan sarrafa ma’adinai, da hada kayayyaki daban daban. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link