Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, ta amince za ta biya dukkanin kuɗaɗen jinyar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Nata’ala, wanda ke fama da ciwon daji.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne, ya bayyana haka lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke Potiskum.
Ya ce gwamnatin za ta haɗa kai da asibitin da yake jinya domin tabbatar da ya samu kulawa ta musamman.
Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan alheri na nuna yadda Gwamna Buni ke tausaya wa jama’arsa tare da taimaka wa masu buƙatar kulawar gaggawa.
Wannan kuma ya nuna jajircewar gwamnatin wajen inganta harkar lafiya da tallafa wa jama’a.
Malam Nata’ala ya yi wa Gwamna Buni godiya bisa wannan taimako, inda ya ce hakan zai zama babban sauƙi a gare shi da iyalinsa.
Ya yi addu’ar Allah Ya saka wa gwamnan da alheri tare da ci gaba da kare shi.
A farkon wannan mako ne, Malam Nata’ala ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar Nijar, ya taimaka masa da kuɗi kimanin Naira miliyan 27 domin ya ci gaba da neman magani, bayan ya nemi taimakon jama’ar gari.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link