Sojoji sun yi jana’izar dakarun da Boko Haram ta kashe a Borno

[ad_1]



Rundunar Sojin Najeriya ta yi jana’izar wasu dakarunta da suka rasa rayukansu yayin artabu da ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.

An gudanar da jana’izar ne a maƙabartar barikin soji ta Maimalari da ke Maiduguri.

A cikin wata sanarwa, kakakin Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce kwamandan rundunar, Abdulsalam Abubakar, ya bayyana lamarin a matsayin abu mai raɗaɗi kan sadaukarwar da sojoji ke yi domin kare ƙasa.

Ya ce dakarun da suka rasu sun nuna jarumta da jajircewa wajen hidimtawa ƙasa.

A cewarsa, mutuwarsu babbar rashi ce ga iyalansu, rundunar sojin Najeriya da kuma ƙasar baki ɗaya.

Kwamandan ya kuma bai wa iyalan sojojin tabbacin cewa rundunar za ta tallafa musu, tare da tabbatar da cewa za a biya dukkanin haƙƙoƙin da suka dace ga iyalan mamatan.

Shi ma gwamnann Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ta bakin wakilinsa Mustapha Ali Yabe, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da rundunar sojin Najeriya.

Ya kuma ce Gwamnatin Jihar Borno za ta ci gaba da tallafa wa sojoji da iyalan jaruman da suka rasa rayukansu wajen kare Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *