Aminu Ado ya sanar da ’yan sanda shirin gudanar da hawan salla a Kano

[ad_1]



Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, cewa ta fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Hawan Salla idan an kammala azumin watan Ramadan.

Wannan na cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 7 ga watan Maris, 2026, wadda aka aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori.

Fadar ta ce za a gudanar da bukukuwan hawan sallar daga fadar sarkin da ke unguwar Nassarawa a Kano.

Sakataren Sarkin, Abdullahi Haruna Kwaru ne, ya sanya wa wasiƙar hannu, inda ya ce Sarkin da mambobin majalisar masarautar sun amince da shirye-shiryen bukukuwan.

A cewar fadar, bukukuwan sallar za su haɗa da hawan hawan salla, hawan Daushe, hawan Nassarawa, da hawan Fanisau

Fadar ta ce an tura wa jami’an tsaro cikakken bayanai game da ranakun gudanarwa, lokaci da wuraren da za a yi hawan.

Ta kuma ce Sarkin da majalisar masarautar suna godiya ga jami’an tsaro kan haɗin gwiwar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.

Fadar ta kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da nasarar gudanar da bukukuwan salla a faɗin jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *