Babu Sihiri A Nasarorin Da Manchester City Ke Samu A Baya Bayan Nan – Guardiola

[ad_1]

Daga Rabilu Sanusi Bena

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewar masu horar da kwallon kafa ba za su yi sihiri domin kawai su samu nasara a wasanni ba.

Guardiola ya bayyana hakane bayan nasarar da City ta samu akan Nottingham Forest a Makon da ya gabata, kwallon da Rayan Cherki ya ci a karshen mako ta sa City tayi nasara da ci 2-1 akan Nottingham Forest ranar Asabar, wadda ta mayar da su kan teburin firimiya na ɗan wani lokaci.

Arsenal ta sake ɗarewa akan teburin gasar Firimiya bayan samun nasara akan Brighton da ci 2-1, inda City ta koma matsayi na biyu da maki biyu tsakaninta da Arsenal, City ta kare a matsayi na uku a kakar wasa ta bara, maki 13 a bayan zakarun gasar Liverpool, bayan sun lashe kofuna hudu da suka gabata.

Nasara daya a wasanni 13 ciki har da rashin nasara sau biyar a jere tsakanin watannin Oktoba da Nuwamba da Manchester City tayi fama dashi ya janyo cece-kuce akan yadda ake tafiyar da kungiyar, sannan kuma Manchester City ta sha kashi a hannun Real Madrid a wasan zagayen sili daya na gasar Zakarun Turai, ficewarsu ta farko a wannan matakin tsawon shekaru 12.

Guardiola ya ce “Manajoji ba masu sihiri ba ne, kawai muna yanke shawarar yadda za a taka leda, mu saka ‘yan was, sannan mu ga yadda za ta kaya” ya cigaba da cewa, “wani lokaci ana bukatar lokaci, a kakar wasa ta karshe da muka buga, sau nawa, ni da kaina ina sukar yanayin da kungiyar ciki”, in ji Guardiola.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *