An kama tsohon kansila da kilo 40 na tabar wiwi a Legas
[ad_1]
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun kama wani tsohon kansila a Jihar Legas kuma mataimaki na musamman ga wani ɗan majalisa, bayan da suka gano kilo 40 na tabar wiwi nau’in skunk a gidansa da ke Ilado a yankin Ibeju-Lekki.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana a wata sanarwa ranar Lahadi cewa wanda ake zargin mai suna Sheleru Sadiq Olalekan mai shekara 45, an kama shi ne bayan da jami’an hukumar suka kai samame gidansa sakamakon sahihan bayanan sirri da suka samu.
A cewarsa, an gano miyagun ƙwayoyin a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, inda a yayin tambayoyi, Olalekan ya amsa cewa ƙwayoyin da aka samu nasa ne kuma gidan da aka same su a ciki nasa ne.
NDLEA ta ce Olalekan ya kuma tabbatar da cewa ya taɓa yin wa’adin mulki biyu a matsayin kansilan da ya wakilci al’ummar Orimedu a Ƙaramar Hukumar Ibeju-Lekki.
A wani samame na daban a Abuja kuwa, jami’an NDLEA sun kama wani ɗan kasuwa mai shekara 32, Emeka Hyginus Okwor, wanda ke tafiya daga Obollo-Afor a Jihar Enugu zuwa Zuba a Babban Birnin Tarayya.
Binciken da aka yi a kayansa ya nuna an ɓoye ƙwayoyi 1,000 na tapentadol a cikin ƙunzugun jarirai.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana kai kwayoyin ne zuwa ƙauyen Guduwa da ke Ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja, inda yake gudanar da wani shagon sayar da kayan abinci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link