Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana
[ad_1]
Dan wasan baya na tawagar Super Eagles na Nijeriya Calvin Bassey, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa tawagar tana da karfin da za ta iya lashe gasar cin kofin kasashen Afirka ta bana 2025 da za a buga a Morocco, dan wasan maybe shekaru 25 dake taka leda a Fulham, wanda ya buga kowanne minti na wasannin share fagen shiga gasar cin kofin Duniya da Nijeriya ta buga kwanan nan, ya yi imanin cewa abinda ya faru a shekarar 2023 a Ivory Coast ya karawa tawagar kwarin gwuiwa.
Bassey ya fadi haka a wata hira da ya yi da Fulham TV kwanan nan, lokacin da aka tambaye shi ko wannan tawagar za ta iya lashe gasar, yace “Kofin AFCON da aka buga na karshe 2023, inada shekaru 23 amma wannan lokacin na Kara shekaru tareda dabara kamar dai sauran yan wasan dake cikin tawagar, da yawa daga cikin kungiyar sun girma kuma mun sami kwarewa sosai fiye da lokacin baya”.
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta fara wannan gasa ba tareda manyan yan wasanta biyu ba, Troost Ekong da Ahmed Musa sun yanke shawarar yin Ritaya daga wakiltar Nijeriya a matakin kasa bayan shafe tsawon shekaru, ana sa ran cewa kambun kyaftin din zai koma ga dan wasan tsakiya Wilfred Ndidi, wanda kocin ya amince da muhimmiyar rawar da yake takawa a yanzu.
Nijeriya tana rukunin C, inda za ta buga dukkan wasanninta a filin wasa na Fez, kasar dake Yammacin Afirika na neman lashe gasar AFCON karo na hudu, Nijeriya tayi rashin nasara a wasan karshe da ci 1-0 a hannun masu masaukin baki Ivory Coastya a wasan da aka buga a shekarar 2023.
[ad_2]
Source link