Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 5, sun ceto mutum 3 a Borno




Sojojin rundunar Operation HADIN KAI sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da ceto wasu mutum uku da aka sace a Jihar Borno.

An kai samamen ne da safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Janairu, 2026, a Ƙaramar Hukumar Konduga.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar a Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

A cewarsa, sojojin sun yi aiki tare da ’yan sa-kai, inda suka yi artabu da ’yan ta’addan a kan hanyar Sojiri.

A yayin artabun, an kashe ’yan ta’adda biyar, amma baby wanda ya rasa ransa a cikin sojojin ko ’yan sa-kai ba.

Laftanar Kanar Uba, ya ce sun ceto mutum uku; maza biyu da mace ɗaya, kuma an ƙwato bindigogi ƙirar AK-47.

Ya ƙara da cewa nasarar ta nuna ƙarfin haɗin gwiwa tsakanin sojoji da al’umma, da kuma ƙudirin rundunar na kare al’umma da murƙushe ’yan ta’addan.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da matsa wa ’yan tada ƙayar baya har sai zaman lafiya ya samu a yankin Arewa maso Gabas.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *