Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani

[ad_1]



Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki.

A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya.

A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane.

A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali.

Umarnin ya kuma bayyana cewa duk wani babban mutum da ke buƙatar tsaro zai nemi jami’an hukumar tsaron fararen kaya (NSCDC).

Sai dai a martaninsa a shafinsa na X, Sanata Sani ya nuna damuwa cewa wannan umarni na iya zama magana kawai ba tare da cikakken aiwatarwa ba.

Ya rubuta cewa: “Janye ’Yan Sanda daga manyan mutane ra’ayi ne mai kyau da kuma kyakkyawan tsari duba da gaggawar buƙatun tsaron ƙasa, amma zai iya farawa kuma ya ƙare a matsayin magana kawai.”

Najeriya ta sake fuskantar tashin hankali, ciki har da hare-haren Boko Haram a Borno da kuma farmakin ’yan bindiga a jihohin Kebbi, Neja, Kwara da Borno da Bauchi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *