Minista ya gayyaci hafsoshin tsaro saboda yawaitar hare-hare
[ad_1]
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gayyaci dukkanin shugabannin rundunonin sojoji taro saboda yawaitar hare-haren da ake kai wa sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.
An gudanar da taron ne a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.
Sauran sun haɗa da Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, da Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Idi Abass, da kuma wakilai daga Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), da sauran su.
Aminiya ta ruwaito yadda a baya-bayan nan ’yan ta’adda sun kashe aƙalla kwamandojin rundunar sojoji uku masu muƙamin Laftanar-Kanal a Jihar Borno.
Baya ga waɗannan kwamandoji da aka kashe, wasu sojoji da dama ma sun rasa rayukansu.
Haka kuma ’yan ta’addan sun sace ɗaruruwan mutane a wasu hare-hare da suka kai a baya-bayan nan.
Da yake magana game da taron, Ministan Tsaron ya ce sun amince za su sake duba dabarun da ake amfani da su wajen yaƙi da ’yan ta’adda.
Ya ce: “Mun san cewa an yi asara a ɓangarenmu, amma asarar ta fi yawa a ɓangaren ’yan ta’adda,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link