EFCC ta ƙwace gidajen Malami a Abuja




Jami’an Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa sun yi wa gidajen tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami ƙawanya a wani yunkuri na ƙwace muhallin tsohon Babban Lauyan na Najeriya.

Tun dai a ranar Litinin da ta gabata ce jami’an EFCCn suka ka ziyarci wasu gidajen tsohon ministan da ke Maitama a Abuja, da zummar rufe bisa abin da suka bayyana a matsayin aiwatar da umarnin kotu.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an EFCC sun je wuraren ne da safiyar ranar, inda suka sanya alamar hattara da haramta amfani da gine-ginen, duk da ƙorafin Malami kan sahihancin umarnin kotun da jami’an suka gabatar.

Malami ya ce umarnin kotun da aka bayar tun a ranar 6 ga Janairu, 2026 na wucin gadi ne na tsawon kwanaki 14 kacal, wanda a cewarsa ya riga ya ƙare, kuma ya ƙalubalanci matakin a gaban kotu.

“Mun riga mun mayar da martani kan umarnin kotun, kuma muna jiran hukunci. Don haka amfani da umarni da wa’adinsa ya ƙare ba daidai ba ne,” in ji shi yayin wata hira da ya yi da tashar Channels TV.

Sai dai jami’in EFCC ya nace cewa suna da hurumin yin hakan muddin kadarorin suna ƙarƙashin binciken ƙwacewa, yana mai cewa umarnin da suka gabatar ya ba su damar ɗaukar matakin.

Zarge-zargen da ake yi masa

Ana zargin Abubakar Malami da hannu a wasu laifuka da suka haɗa da safarar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da suka kai biliyoyin naira, tare da saye da mallakar kadarori a jihohin Kebbi, Kano da Abuja.

A cewar gwamnati, Malami da wasu na kusa da shi sun ɓoye yadda suka samu wasu kuɗaɗe da suka haura biliyan N1, tare da amfani da su wajen sayen gidaje da kadarori a wurare daban-daban.

Haka kuma ana zarginsa da amfani da wasu kamfanoni wajen ɓoye asalin kuɗaɗen, da kuma amfani da su a matsayin jinginar bashi a banki.

Shari’a da DSS

Baya ga wannan, Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ma ta gurfanar da Malami da ɗansa a gaban kotu kan zargin tallafa wa ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ra’ayoyin masana

Wasu lauyoyi sun bayyana cewa duk wani umarnin kotun muddin wa’adinsa ya ƙare, ba za a iya aiwatar da shi ba sai an sabunta shi.

Wani lauya, Godwin Ijunbor, ya ce aiwatar da umarni da wa’adinsa ya ƙare na iya zama doka ta haram, yayin da wani lauya, Chibueze Maduka, ya jaddada cewa dole ne a sabunta umarnin kafin a yi amfani da shi.

A nasa ɓangaren, wani malamin kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja, Farfesa Sadiq Abubakar, ya bayyana matakin ƙwace gidajen ministan a matsayin mai ɗauke da alamun siyasa da kuma yiwuwar cin zarafin, yana mai kira ga hukumomi su bi doka da oda.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *