HOTUNA: Shettima, NSA, Gwamnoni sun halarci addu’a ta musamman da aka shirya wa Tinubu
Manyan ’yan siyasa da malaman addini sun taru a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, domin yi wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, addu’a yayin da ya cika shekaru 74.
Daga cikin waɗanda suka halarta taron addu’ar akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da ’yan majalisun tarayya, da kuma gwamnonin jihohi sama da 10, ciki har da Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Malaman addinin Musulunci ne suka jagoranci addu’ar, inda suka roƙi Allah Ya bai wa shugaban ƙasa hikima da karfin gwiwa wajen tafiyar da harkokin ƙasa.
Sun kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Najeriya, tare da kira ga shugabanni su yi mulki bisa adalci da riƙon amana.
Wannan taro na daga cikin shirye-shiryen bikin cikar Shugaba Tinubu shekaru 74, wanda ya dace da al’adar gudanar da addu’o’i a irin waɗannan muhimman lokuta.
Ga hotunan yadda taron ya gudana: