Kotu ta ƙi ba da belin El-Rufai
[ad_1]
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, bayan da aka gurfanar da shi a gabanta a ranar Talata.
Lauyoyinsa sun buƙaci kotun da ta ba shi beli, amma lauyoyin Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ICPC da ke ƙarar sa, sun buƙaci a ci gaba da tsare shi.
A cewar lauyoyin na ICPC, zarge-zargen da ake yi masa na da nauyi, kuma bayar da shi beli na iya kawo tsaiko ga binciken da suke ci gaba da gudanarwa.
Daga ƙarshe, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekara.
Tun dai ranar 19 ga watan Fabrairu ne tsohon gwamnan jihar na Kaduna ke riƙe a hannun hukumar ICPC bayan da ta kama shi jim kaɗan bayan hukumar EFCC ta sake shi.
A ranar 5 ga watan Maris ne wata kotun majistire ta bai wa ICPC damar tsawaita tsare El Rufai da mako biyu.
A wata sanarwar da ICPC ta fitar a jiya Litinin kan gurfanar da shi a gaban kuliya, hukumar na tuhumar El-Rufai da zarge-zarge da dama da suka haɗa da karkatar da kadarorin gwamnati da mallakar kadarorin jama’a ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗaɗen haram.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link