Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Daga Hannun Ƴan Fashi, Sun Kama Mutane 6 A Nasarawa
[ad_1]
Rundunar ƴansandan Jihar Nasarawa ta ceto mutane uku da aka sace a ƙaramar hukumar Lafia ta jihar. Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata biyu da namiji guda, inda aka kuɓutar da su daga ƙauyukan Angara da Fadaman Bauna.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa jami’an sashen ƴansanda na Assakio ne, tare da haɗin gwuiwar ƴan banga ne suka gudanar da aikin ceton. Ya ce bayan kuɓutar da su, an kai waɗanda abin ya shafa duba lafiyarsu sannan aka miƙa su ga iyalansu.
- Zan Tabbatar Duk Ƴan Dakon Hatsi A Nassarawa Sun Mallaki Katin Zaɓe — Alhaji Danji
- Yadda Dauda Lawal Ya Dukufa Wajen Farfado Da Darajar Jihar Zamfara
SP Nansel ya ƙara da cewa lamarin ya biyo bayan ƙorafin da al’ummar yankin suka kai wa ansanda, inda suka sanar da cewa wasu da ake zargi sun shiga ƙauyen Angara suka sace mata biyu, suka bar jariri a wurin, sannan daga bisani suka sake sace wani namiji a ƙauyen.
Bayan samun bayanan, kwamishinan ƴansandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin kamo masu laifin, wanda hakan ya kai ga cafke mutane shida da ake zargi da aikata laifin. Rundunar ta ce waɗanda aka kama sun amsa laifinsu, kuma an miƙa su zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kotu, tare da jaddada ƙudirin ƴansanda na ci gaba da yaƙar aikata laifuka a faɗin jihar Nasarawa.
[ad_2]
Source link