Hukumar NDLEA Ta Kama Mutum 1,130 Da Kwato Miyagun Kwayoyi Kilo 9,402 A 2025 A Kaduna


Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Kaduna ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da shan miyagun kwayoyi da fataucinsu a cikin shekarar da ga gabata ta 2025, inda ta yi nasarar kama kwayoyi tare da cafke mutane da dama, da lalata wuraren boyewa da sayar da miyagun kwayoyi a fadin Jihar Kaduna.

Kwamandan hukumar na Jihar Kaduna, CN Mohammed Tukur, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a Kaduna.

  • Yadda Dauda Lawal Ya Dukufa Wajen Farfado Da Darajar Jihar Zamfara
  • An Gudanar Da Taron Shawarwari Kan Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

Kwamanda Tukur ya bayyana cewa rundunar ta kara tsaurara sa ido da kai hare-hare da kuma aiwatar da ayyukan tattara bayanan sirri, bisa umarnin Shugaban NDLEA da kuma kudirin Gwamnatin Jihar Kaduna na kare lafiyar al’umma da tabbatar da tsaro.

Ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Disamba 2025, rundunar ta cafke mutane 1,130 bisa laifuffukan da suka shafi miyagun kwayoyi, inda maza 942 da mata 188 ke cikin wadanda aka kama.

Kazalika, jami’an NDLEA sun kwato miyagun kwayoyi masu nauyin kilo 9,402.506, ciki har da hodar ibilis da magungunan kwakwalwa da sauran manyan miyagun kwayoyi.

A kokarin da ake ci gaba da yi na tarwatsa hanyoyin rarraba miyagun kwayoyi a matakin kananan hukumomi, rundunar ta lalata wuraren sayar da miyagun kwayoyi 486 da aka gano a fadin Jihar Kaduna. Haka kuma, an gurfanar da mutane 246 a gaban kotu, yayin da bincike kan sauran shari’o’i ke ci gaba.

Kwamandan ya kara da cewa jami’an rundunar sun kwato makamai masu hadari yayin wasu ayyuka, ciki har da bindigar AK-47 guda da harsashi 13 masu rai, lamarin da ke nuna alakar da ke tsakanin fataucin miyagun kwayoyi da aikata laifuka masu tashin hankali.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *