Kasar Sin Ta Ce Wajibi Ne A Kare Halastattun Muradunta A Venezuela
[ad_1]
A yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, Venezuela kasa ce mai cikakken ‘yanci wacce ke da cikakken ‘yancin kai na dindindin a kan albarkatun kasa da dukkan harkokin tattalin arziki na yankunanta.
A cewar Mao, dole ne a kare hakkoki da muradun sauran kasashe a Venezuela, ciki har da na kasar Sin.
Mai magana da yawun ma’aikatar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da matakin sojin da Amurka ta dauka a kan Venezuela da kuma bukatarta ta “fifita Amurka a kan komai” idan ana batun Venezuela ta tafiyar da albarkatun man fetur dinta.
Ta ce matakin da Amurka ta dauka, wanda karara na cin zarafi ne, ya saba wa dokokin kasa da kasa sosai, da keta ‘yancin kan Venezuela, da kuma keta hakkin al’ummar Venezuela, kamar yadda ta bayyana a taron manema labarai na yau da kullum. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link