Dalilin da Rasha za ta ci gaba da bai wa bunƙasa makaman nukiliya fifiko — Putin

[ad_1]



Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya bayyana cewa bunƙasa makaman nukiliyar ƙasarsa ya zama “babban abin fifiko matuƙa”, musamman bayan ƙarewar yarjejeniyar nukiliya ta ƙarshe da ke tsakaninta da Amurka.

Putin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar a yayin bikin Ranar Kare Ƙasa ta Rasha, wadda ake amfani da ita wajen nuna ƙarfin soja da ƙarfafa kishin ƙasa.

Ya ce, “Bunƙasa tsarin makaman nukiliya guda uku wanda ke ƙara tabbatar da tsaron Rasha da daidaiton ƙarfi a duniya, shi ne babban abin fifiko a gare mu.”

Putin ya ƙara da cewa Rasha za ta ci gaba da ƙarfafa sojojinta na ƙasa da na ruwa, tare da amfani da ƙwarewar da ta samu daga yaƙin da ta shafe kusan shekaru huɗu tana yi da Ukraine.

A cewarsa, za a inganta dukkan ɓangarorin rundunar sojin ƙasar, ciki har da shirye-shiryen yaƙi, saurin motsi da kuma iya aiki a kowane irin yanayi, ko da kuwa mawuyaci ne.

Maganganun na Putin na zuwa ne kwanaki kaɗan gabanin cika shekaru huɗu da Rasha ta ƙaddamar da farmaki kan Ukraine, yaƙin da ya jawo asarar rayuka da dama tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

A halin yanzu, Rasha da Amurka, waɗanda su ne manyan ƙasashen da ke da makaman nukiliya a duniya, ba su da wata yarjejeniyar sarrafa makaman nukiliya da ke ɗaure su, bayan ƙarewar yarjejeniyar New START a farkon wannan wata.

Sai dai Moscow ta ce za ta ci gaba da bin mataki na “hankali da ɗa’a” wajen sarrafa makaman nukiliyarta, tare da mutunta iyakokin da aka gindaya wa ajiyar makaman.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *