“Ku Biya Mu Naira Miliyan 100 Ko Mu Kawo Muku Hari” – ‘Yan Bindiga Ga Al’ummar Kebbi

[ad_1]

‘Yan bindiga a sassan Kudancin Kebbi sun nemi Naira miliyan 100 daga al’ummar Utouno da ke karamar hukumar Ngaski, inda suka yi musu barazanar kai hare-hare idan ba a biya musu bukatarsu ba.

An rahoto cewa, ‘yan bindigar sun yi barazanar ne ta hanyar turo da wasika zuwa ga shugabannin al’ummar.

  • EFCC Ta Cafke Mutane 20 A Zaɓen FCT, Ta Kwato Sama Da Miliyan 17 Wajen Masu Sayen Ƙuri’a
  • Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas

Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun fargabar tsaro a sassan Kebbi da jihohin makwabta, inda kungiyoyin ‘yan ta’addar ke kai munanan hare-hare, sace-sacen mutane, da dabbobi a yankunan karkara.

A cikin wasikar, kungiyar ta gargaɗi mazauna yankin da kada su yi dauki wasikar da wasa.

“Wannan ba wasa ba ne. Dole ne ku biya mu Naira miliyan 100. Idan kun ki, za ku fuskanci sakamakon kuma kada ku zargi kowa sai kanku. Ko da kun kira sojoji, ba za su iya hana mu ba,” in ji wasikar.

Kungiyar ta kuma ambaci wani hari da aka kai wa al’ummar Woro a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, inda aka ruwaito an kashe mutane da dama bayan sun yi watsi da irin wannan gargadin.

Mazauna yankin, ta hannun Jaridar Daily Trust, sun tabbatar da karɓar wasikar, wadda suka ce ta jefa al’ummar cikin firgici.

Wani mazaunin yankin, Abbas Alkali, ya ce, “Eh, sun rubuto mana wasika suna neman Naira miliyan 100 daga al’ummarmu. Yanzu kowa cikin firgici yake rayuwa saboda barazanar kai mana hari idan muka kasa biyan bukatarsu.

“An kai rahoton lamarin ga shugaban karamar hukumar, kuma na ji cewa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna daukar matakai don magance barazanar.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *