Babu Tabbacin Za Mu Iya Gudanar Da Sahihin Zaɓe A 2027 —Shugaban INEC
[ad_1]
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya ce babu tabbacin ko hukumar zaɓe za ta iya gudanar da sahihin zaɓe mai cike da nasara 100 bisa 100 a 2027 ko da ta saka sakamakon zaɓen a na’ura.
Amupitan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ƙungiyar farar hula ta mai neman a inganta harkokin zaɓe ta shirya, wanda aka gudanar a Otel ɗin Abuja Continental, a ranar Lahadi da ta gabata.
A cewarsa, zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance mafi kyau a tarihin Nijeriya.
Ƙungiyoyin farar hula da masana harkokin zaɓe da masu sa ido a cikin harkokin zaɓe da kuma wakilan al’umma na daga cikin waɗanda suka halarci a taron don tattauna al’amuran da suka shafi zaɓe.
- Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
- Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci Ta Sake Neman A Cire Shugaban INEC
Sai dai kuma Amupitan ya ce Nijeriya na buƙatar yin amfani da sauƙaƙan dokar harshe, inda zai yi saukin fahimta ga kowane ɗan Nijeriya tare da yaba wa kowane sashe na dokar zaɓe ta 2026.
Ya ce a yayin zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Abuja, sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi biyar an bayyanasu a kan lokaci, amma sakamakon zaɓe ƙaramar hukumar Kuje bai bayyana kan lokaci ba har sai da ya kai rana ta gaba.
Amupitan ya ƙara da cewa ya kamata a tabbatar da cewa zaɓe mai nasara ya dogara ne kan kammala tsarin kayan aiki.
Amupitan ya ce, “Na farko, idan kana son auna ko zaɓen ya yi nasara, dole ne ka tantance ko an fara zaɓen kamar yadda aka sanar. Kuma mun sanar da zaɓen da ƙarfe 8.30. Don haka idan mun iya fara zaɓen da ƙarfe 8.30 shi ne za mu iya samun nasara.
“Na biyu, idan zaɓen ya kasance cikin lumana. Na uku, idan muka iya sarrafa sakamakon zaɓen yadda ya kamata, sannan a bayyanar da sakamakon, to za ka iya cewa ka yi zaɓe mai nasara.
“A matsayinmu na hukumar da ke sa ido, mun ƙudiri aniyar cimma duk wannan nasarar.
“Amma duk da haka, dole mu yarda cewa akwai wasu matsalolin kayan aiki, wasu kuwa na Ɗan’adam ne, kuma muna ƙoƙarin magancesu. Bari in roƙi ‘yan Nijeriya, saboda na lura yanzu cewa abin da ‘yan Nijeriya suke so shi ne, sahihin zaɓe. Zan yi ƙoƙarina daidai gwargwadon ikona don ba wannan ƙasa zaɓe mafi kyau.
“Watakila ba za mu iya samun zaɓen kashi 100 cikakke a yanzu ba. Amma dangane da isar da sakamakon ta hanyar na’ura, na riga na faɗa a gabanin zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Abuja cewa muna da ikon isar da sakamakon ta na’ura, kuma za mu sanar da sakamakon ta na’ura.
“Abin da kawai ke damunmu shi ne, lokaci na haƙiƙa. Mene ne lokaci na haƙiƙa? Misali, idan ka tafi, ka yi amfani da manhajarka don tura kuɗi daga asusunka. Ko a cikin birnin Abuja, ka tura naira 50,000 zuwa ga Mista B, kuma daga manhajarka, kuɗin ya tafi.
“Amma mutumin bai ga kuɗin ba har sai bayan wasu mintuna 30, wani sa’a, ko ma da yamma. Don haka waɗannan wasu ne daga cikin abubuwan. Kuma lokacin da ka ce lokaci ne na haƙiƙa, da zarar an gama, dole ne a karɓa.
“Saboda haka, gudanar da sakamakon zaɓe da kayan aiki su ne manyan batutuwa guda biyu da, daga ɓangarenmu, muna ƙoƙarin ganin yadda za mu iya gudanar da su sosai, domin inganta gaskiya da amincin tsarin.
“An kawar da matsalar na’ura. Na’ura ba zai sake kawo matsala ba a zaɓen Nijeriya, kuma duk lokacin da na kalli sashe na 63 na dokar zaɓe, ko a zaɓen ƙananan hukumomin abuja, ban da wannan jinkiri, ba mu samu wata matsala ta na’ura ba, ma’ana cewa kwai an samar da ita ne don kariya. Kuma a lokacin mulkina, ba za ta gaza ba.
“Ko da ta gaza, dole ne a sanar da sakamakon zaɓe. Amma matsalar kaɗai ita ce, idan ta gaza sanar da sakamakon zaɓe a kan lokaci, kamar yadda muka samu a wancan ƙaramar hukuma.
“Wannan shi ne babban matsala. Yanzu da haka da nake yin magana game da magance matsalar, zaɓe yanzu, ko da yaushe, yana da nasaba da fasaha. Amma kafin ka yi amfani da kowace fasaha, yana da muhimmanci ka gwada wannan fasaha sosai.
“Don haka bincikena na zaɓen 2023 shi ne yayin da aka gwada na’urar a cikin jihohi, alal misali zaɓɓen Osun, zaɓen Ekiti, duk da haka, lokacin da ya zo ga zaɓen tarayya, musamman zaɓen shugaban ƙasa wanda yanzu ya zama na tsakanin jihohi, ba a gwada shi yadda ya kamata ba.
“Don haka, ɗaya daga cikin abubuwan da muke ƙoƙarin yi kafin zaɓen shi ne, tabbatar da cewa an sanar da sakamakon zaɓen ta na’ura a dukkan faɗin jihohin ƙasar nan.
“Da yardar Allah, zaɓen shekarar 2027 zai kasance mafi kyawun zaɓen da ‘yan Nijeriya za su yi. Domin ‘yan Nijeriya a 2023 sun sha bamban da abin da za ku samu a 2027. Mutane sun ƙara samun wayewa sosai.”
[ad_2]
Source link