Mun nutsar da jiragen ruwan Iran sama da 30 — Amurka
[ad_1]
Wani babban jami’in sojan Amurka ya bayyana cewa, Amurka ta nutsar da jiragen ruwan yaƙi na Iran sama da 30 a lokacin da ake tsaka da gudanar da yaƙin, yayin da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa daga dakarun Tehran suka ragu sosai.
“Yanzu haka mun nutsar da jirage sama da 30, kuma a cikin ’yan sa’o’in da suka gabata, mun harba makami kan wani jirgin ruwan Iran mai ɗauke da jirage marasa matuƙa, wanda girmansa ya kusa kai na jiragen dakon jiragen sama na Yaƙin Duniya na Biyu. Kuma a halin yanzu jirgin yana ci da wuta,” in ji Admiral Brad Cooper a wani taron manema labarai.
A halin da ake ciki, Cooper, wanda shi ne shugaban rundunar tsakiya (Central Command) mai lura da dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya, ya ƙara da cewa: “Hare-haren makaman linzamin Iran sun ragu da kashi 90 cikin 100 tun daga ranar farko.
Hare-haren jirage marasa matuƙa kuma sun ragu da kashi 83 cikin 100.”
Amurka ta ƙaddamar da gagarumin harin sama kan Iran tare da haɗin gwiwar dakarun Isra’ila a ranar 28 ga watan Fabrairu, inda Iran ta mayar da martani ta hanyar harba ɗaruruwan jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami ga sauran ƙasashen yankin.
Lalata ƙarfin makaman linzamin Iran da rundunar dakarun ruwanta na ɗaya daga cikin manyan manufofin da Washington ta ayyana na wannan farmaki, wanda Amurka ta sanya wa suna “Operation Epic Fury” ( Zazzafan Fushi).
Cooper ya ce Amurka ba wai kawai tana kai hari ne kan makaman linzamin Iran ba, har ma tana ƙoƙarin “rushe dukkan masana’antun ƙera makaman linzamin ƙasar.”
“Yayin da muke matsawa zuwa mataki na gaba na wannan aiki, za mu bi mataki-mataki wajen ruguza ƙarfin ƙera makaman linzamin Iran na nan gaba,” in ji Admiral din.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link