Mutane 20 sun mutu bayan jirgin soji ɗauke da kuɗi ya faɗi a Bolivia
[ad_1]
Aƙalla mutane 20 ne suka rasu yayin da wani jirgin sojin Bolivia mai ɗauke da kuɗaɗe ya yi hatsari a lokacin sauka kusa da babban birnin ƙasar, La Paz, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar ranar Juma’a.
Jirgin, samfurin C-130 Hercules wanda kamfanin Lockheed Martin ya ƙera, ya kauce daga hanyar sauka a filin tashi da saukar jirage na El Alto, inda ya faɗi kan wata babbar hanya, lamarin da ya lalata motoci da dama tare da jikkata wasu mutanen.
Rahotanni sun nuna cewa kuɗaɗen da jirgin ke ɗauke da su sun warwatse, lamarin da wasu mutane suka daka wawaso a ƙoƙarin kwashe su.
Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suka daka wawa, sannan daga bisani suka ƙone kuɗaɗen a wurin domin hana satar su.
Wata ‘yar kasuwa mai suna Cristina Choque ta ce wani ɓangare na jirgin ya faɗo kan motarsu, inda ‘yarta ta ji rauni a kai.
Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta bayyana cewa za a buɗe bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Haka kuma, hukumomin lafiya sun ce aƙalla mutane 28 sun jikkata, yayin da asibitoci a El Alto suka buɗe ƙofar neman tallafin jini domin kula da majinyata.
Hukumomin shari’a sun kuma ce an kama mutane 12 da ake zargi da satar kuɗi a cikin rikicin da ya biyo bayan hatsarin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link