Gwamna Abba Ya Kammala Shirye-shiryen Komawa APC A Ranar Litinin

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, na shirin sauya sheƙa zuwa APC a ranar Litinin.

Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a halin yanzu da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, yanzu haka yana Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya sheƙarsa.

  • Tashar Jiragen Ruwa Ta Lekki Ta Fara Tarbar Kwantaina Daga Kasashen Afirka
  • Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arzikin Teku Ta Kaddamar Da Sabuwar Fasaha Don Janyo Masu Zuba Jari

Majiyoyi sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da manyan shugabannin APC ne za su tarɓe shi.

Haka kuma, an sanar da manyan shugabannin jam’iyyar APC a Kano, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, domin taka rawa a wannan tsari.

Tun da farko Shugaba Bola Tinubu bai amince da sauya sheƙar gwamnan ba tare da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.

Sai dai bayan yunƙurin shawo kan Kwankwaso ya ci tura, rahotanni sun ce shugaban ya amince da karɓar Abba zuwa APC.

Matakin gwamnan ya haifar da ruɗani a tsarin Kwankwasiyya, inda magoya baya da dama suka nuna ɓacin ransu tare da jaddada biyayyarsu ga Kwankwaso, lamarin da ke nuna babban sauyi a siyasar Jihar Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *