Gwamnan Kano zai sauya sheƙa zuwa APC a ranar Litinin

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP a hukumance domin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Gwamna Abba shi kaɗai gwamna mai ci a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a halin yanzu.

Wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIA cewa tuni gwamnan na Kano, ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen komawarsa APC.

Majiyar ta bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe ne, za su tarbi gwamnan a Abuja.

A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen sauya sheƙarsa, an kira tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, daga tafiyar da ya yi zuwa Dubai.

Haka kuma, an umarci shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ya dawo Najeriya daga tafiya Saudiyya da ya yi domin yin Umrah.

Ana sa ran zai miƙa wa Gwamna Abba katin zama ɗan jam’iyyar APC a mazaɓarsa ta Diso da ke Ƙaramar Hukumar Gwale da ke Kano, a mako mai zuwa.

Ana kuma sa ran gwamnan zai gana da Ganduje cikin mako mai zuwa domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen ciyar da jam’iyyar gaba a Jihar Kano.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa da farko, Shugaba Bola Tinubu bai amince da sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC ba, ba tare da Sanata Rabiu Kwankwaso ba.

Kwankwaso na da mabiya masu tarin yawa a Jihar Kano da wasu sassan Arewa.

“Da farko shugaban ƙasa ya dage cewa ba zai karɓi gwamnan ba tare da Kwankwaso ba.

“Bayan ƙoƙarin shawo kan Kwankwaso ya ci tura, sai Gwamna Hope Uzodinma ya shawo kan shugaban ƙasa ya amince a karɓi gwamnan,” in ji majiyar.

Tuni masu muƙamai a gwamnatin Kano, suka bayyana goyon bayansu a fili tare da roƙon Gwamna Abba da ya jagorance zuwa jam’iyyar APC.

Tuni dai lamarin sauya sheƙar gwamnan ya haddasa saɓani da rarrabuwar kai a tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya, lamarin da ya sa wasu suke goyon bayan Kwankwaso, yayin da wasu suke ke goyon bayan Gwamna Abba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *