Filin Hakar Mai Da Iskar Gas Na “Deep Sea No.1” Na Sin Ya Kai Matsakaicin Na Filin A Kan Tudu

[ad_1]

Yau Jumma’a, kamfanin samar da man fetur na teku na kasar Sin wato CNOOC, ya sanar da cewa filin hakar mai da iskar gas dake teku mai suna “Deep Sea No.1”, wanda yake filin samar da man fetur mafi girma a kasar Sin, ya kammala jigilar man fetur ta jiragen ruwa guda 100 kwanan nan, daga lokacin da aka fara aikin. A shekarar 2025, yawan man fetur da iskar gas na filin ya wuce tan miliyan 4.5, wanda ya yi daidai da na matsakaicin ma’aunin samar da man fetur na filin dake kan tudu.

Filin iskar gas na “Deep Sea No.1” shi ne filin samar da man fetur da iskar gas mafi zurfin aiki a kasar Sin har zuwa yanzu, kuma mafi girman fuskantar matsin lamba wajen samarwa, kana mafi girman kalubalen bincike da habakawa, sannan mafi girman karfin samar da iskar gas na kasar. Kazalika, shi ne mafi zurfin ruwa wanda aikinsa ya wuce mita 1500, kuma mafi girman zafin yanayi na samarwa inda ya kai digiri 138 a ma’aunin Celsius. An tabbatar da yawan iskar gas dake ajiye a cikin kasa a wurin ya wuce kyubik mita biliyan 150. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *