An bayar da belin Kwamishinan da ake zargi da tallafa wa ta’addanci

[ad_1]



Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu da wasu mutane uku, waɗanda ake tuhumar su da amfani da kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin ta’addanci.

Mai shari’a Emeka Nwite a ranar Juma’a ne ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kuɗi Naira miliyan 500 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

Sai dai Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin a tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali da ke Kuje, a babban birnin tarayya har sai ya cika sharuɗɗan belin.

Alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa, waɗanda za su tsaya wa wanda aka bada belin sai sun mallaki kadarorin a yankunan unguwannin Asokoro, unguwar  Maitama ko Gwarinpa da ke Abuja sannan su bayar da shaidar mallakarsu ga kotun.

Alƙalin ya kuma umurci Adamu ya ajiye fasfo ɗinsa a gaban kotu kuma kada ya fita ƙasar waje ba tare da izini ba, sannan shi da waɗanda za su tsaya masa zai ya bayar da hotunan fasfo nasu guda biyu na baya-bayan nan.

Yayin da yake ba da umarnin cewa, waɗanda za su tsaya masa dole ne su rantse a gaban kotun, alƙalin ya ce an tsara sharuɗɗan belin ne domin tabbatar da gudanar da adalci.

A ranar Laraba ne Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Adamu, tare da Balarabe Abdullahi Ilelah, da Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed, bisa zargin bayar da tallafin aikin ta’addanci na dalar Amurka miliyan 9.7.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *