Gwamnan Gombe Ya Kafa Hukumar Kula Da Wutar Lantarki
[ad_1]
Khalid Idris Doya
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da kafa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Gombe (GOSERC) da Hukumar Fasahar sadarwa da Tattalin Arzikin zamani ta Jihar Gombe (GIDTEC), a wani mataki na karfafa wadannan fannoni, habaka kirkire-kirkire da kuma zurfafa sauye-sauyen tattalin arziki a jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, wanda ya sanar da amincewar gwamnan, ya bayyana cewa nadin da kafa hukumomin ya biyo bayan amincewar Gwamnan ne ga dokokin da suka kafa hukumomin biyu, lamarin daya ba su cikakken goyon bayan doka don gudanar da ayyukansu.
Don haka Gwamna Inuwa Yahayan ya amince da nadin Dakta Usman Abba Arabi a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Gombe (GOSERC) da Dakta Al-Amin Umar Barambu, a matsayin Babban Daraktan na Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani ta Jihar Gombe (GIDTEC).
Arabi da Barambu suna da kwarewa mai yawa da ake bukata don aiwatar da ayyukan sabbin hukumomin da aka kafa yadda ya kamata.
Kirkirar GOSERC ya yi daidai da kudurin gyaran bangaren wutar lantarki na Gwamnan, musamman wajen amfani da damar da Dokar Wutar Lantarki ta kasa ta bayar don karfafa samar da wutar lantarki, da inganta jigila da dillancinta, da jawo hankalin masu zuba jari da kuma fadada damammakin samun ingantacciyar wutar lantarki a fadin Jihar Gombe.
[ad_2]
Source link