Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi
[ad_1]
Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu.
Dakarun sun kuma ceto mutane biyu da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar, an bayyana cewa dakarun sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da sama da ’yan bindiga 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar ɓarna.
Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan harkokin sadarwa da dabarun mulki, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa manema labarai, cewa wannan aiki ya nuna tsayin daka da ƙarfin dakarun tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda.
Ya ce, “Dakarun sun yi aiki tuƙuru don hana ’yan bindigar kutsawa cikin Kebbi. Wannan sumame wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin daƙile ta’addanci da fashi da makami a fadin jihar.
“Sojojin Najeriya suna ci gaba da kai hare-hare a dazuka da yankunan da ke kan iyaka, musamman a dajin Makuku.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link