Sojoji Sun Kama Mutane 58 Kan Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Edo
[ad_1]
Sojoji sun kama mutane 58 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Edo.
An kama waɗanda ake zargin ne a wani wajen haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba a Ososo, ƙaramar hukumar Akoko-Edo.
- Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan Kano, Nasiru Gawuna Ya Fice Daga APC
- Gwamnatin Filato Ta Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 48 A Jos Ta Arewa
Rundunar sojim da ke Auchi ce ta gudanar da aikin.
A cewar Kyaftin Kennedy Anyanwu, an kama waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 1 na rana a ranar 28 ga watan Maris, 2026, yayin wani sintiri da aka yi bisa sahihan bayanai.
Ya ce wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuka a Jihar Edo.
An kama su kuma an miƙa su ga ‘yansanda a Okpella domin ci gaba da bincike.
[ad_2]
Source link