Jama’a sun tsere bayan ’yan bindiga sun kai hari wasu yankunan Filato
[ad_1]
Mazauna yankunan Zurak da Sabon Gari a gundumar Bashar da ke Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato, sun tsere daga gidajensu bayan wasu hare-hare da ’yan bindiga suka kai.
A ranar Litinin, ’yan bindiga a kan babura sun kai farmaki yankunan.
A Zurak, sun kashe soja guda ɗaya da wasu mutum biyar, yayin da kuma sojoji uku suka ɓace bayan harin.
Mazauna yankunan sun ce maharan sun fara kai hari wuraren binciken tsaro, sannan suka shiga cikin gidaje da shaguna, suka banka musu wuta tare da sace kayan abinci.
Bayan hare-haren, an tura ƙarin jami’an tsaro daga garin Wase, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar, zuwa yankunan da abin ya shafa.
Duk da haka, mutane da dama na ci gaba da tserewa zuwa ƙauyen Kampani, wanda ke kusa da Zurak, domin tsira da rayukansu.
An hangi maza, mata da yara suna tafiya ɗauke da kayayyakinsu yayin da suke barin gidajensu.
Wani mazaunin yankin, Ya’u Usman, ya ce mutane sun tsere ne saboda tsoron sake kai musu hari.
“Mun tsere duk da zuwan jami’an tsaro nan. ’Yan bindiga kan zo da yawa su fi ƙarfin jami’an tsaro. Rayukanmu ba su da tabbas. Idan zaman lafiya ya tabbata, za mu koma,” in ji shi.
Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan hare-haren ba.
Wani jami’in soja mai magana da yawun rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin J.A. John, ya ce zai binciki lamarin sannan ya yi ƙarin bayani.
Ƙauyuka da dama a Ƙaramar Hukumar Wase suna fama da hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane a baya-bayan nan.
A watan Disamban 2025, an sace kusan matafiya 28 a ƙauyen Zak yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa halartar Mauludi a ƙauyen Sabon Layi, wanda ke cikin gundumar Bashar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link