Kuncin Rayuwa: Jam’iyyun Adawa Da Kungiyar Kwadago Sun Caccaki Tinubu
[ad_1]
Jam’iyyar ADC ta caccaki gwamntin Shugaban kasa, Bola Tinubu kan kuncin rayuwa a Nijeriya tare da musanta cewa, jam’iyyar APC ta gudanar da sauye-sauyen tattalin arziki na Tinubu, da suka kawo saukin rayuwa.
Sai dai kuma APC ta mayar da martini kan wannan lamari, ta zargi jam’iyyar adawa ta ADC da yaudarar ‘yan Nijeriya ta hanyar zargin Shugaba Tinubu kan kashi 63 na talauci a kasar kamar yadda bincike ya nuna a makon da ya gabata.
- Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin
- Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin
Binciken masu ruwa da tsaki da aka shirya tattaunawa a Abuja, ya nuna cewa yawan talauci a kasa nan ya tashi sosai daga matsakaicin kaso kusan 49.8 cikin dari zuwa kusan 63 cikin dari bayan cire tallafin mai kafin ya dan ragu kadan bayan gabatar da matakai masu tsauri.
Da yake magana kan lamarin, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya jaddada cewa bayanan sun nuna cewa matakin talauci a Nijeriya ya haura zuwa kashi 63 cikin dari, daga kusan kashi 50 cikin dari kafin a cire tallafin mai.
Abdullahi ya tabbatar da cewa rahoton da ya nuna cewa kashi 93 cikin dari na ‘yan Nijeriya suna ganin kasar na tafiya a mummunan hanya ba batutuwan jam’iyyar adawa ba ne kan lamarin.
Ya ce rahotannin sun nuna karara cewa manufofin gwamnatin APC kan tattalin arziki ba sa tafiya kan ceto rayukan ‘yan Nijeriya karkashin mulkin Tinubu.
Mai magana da yawun ADC ya ce maimakon mayar da hankali kan magance talauci da kuncin rayuwa da ya dabaibaye ‘yan Nijeriya a karkashin wannan gwamnati, jam’iyyar mai mulki ta ci gaba da farmakan jam’iyyun adawa tare da yin watsi da ceto rayukan miliyoyin ‘yan kasa.
Ya kara da cewa ba za a iya watsi da gaskiya ta hanyar bayanan jarida ba, yana jaddada cewa rahoton ‘yanci da ya haifar da muhawara yana nuna cewa yawan talauci a Nijeriya ya kai kashi 63 cikin dari, daga kusan kashi 50 kafin a cire tallafin man fetur.
“Wannan na nufin cewa wasu karin miliyoyin ‘yan Nijeriya za a kara tilasta musu shiga cikin talauci a wannana lokacin da aka gabatar da manufofin tattalin arziki da gwamnatin APC ta gaza aiwatarwa.”
ADC ta kara da cewa yayin da APC ke ikirarin cewa ‘yan Nijeriya suna goyon bayan sauye-sauyen da gwamnati Tinubu ta aiwatar a kasar nan, amma kuma bayanan sun nuna akasin haka.
Mai magana da yawun jam’iyyar adawa ya ce binciken masu zaman kansu sun nuna cewa kashi 93 cikin dari na ‘yan Nijeriya suna ganin cewa kasar na tafiya a mummunan shugabanci.
“Kashi tamanin da takwas cikin dari suna bayyana tattalin arzikin kasa a matsayin mara kyau, yayin da kashi 74 cikin dari ke suna rayuwa cikin kangin talauci. Wadannan ba maganganu ne na ‘yan adawa ba. Ra’ayoyin ‘yan Nijeriya ne da kansu ciki har da ‘yan APC.”
ADC ta ce yayin da APC ke dagewa kan cewa wahalar da ‘yan Nijeriya ke sha ta kasance ta wucin gadi ne, said ai kuma alkaluma suna ba da wani labari daban.
“Binciken baya-bayan nan ya nuna cewa kashi 82 cikin dari na ‘yan Nijeriya bas a samun isasshen abinci a kalla sau daya a cikin shekarar da ta gabata, kashi 82 cikin dari na fama da rashin kula da lafiya, kashi 79 cikin dari sun daina amfani da man girki, kashi 74 cikin dari na fama da rashin tsaftar ruwa, kuma kashi 95 cikin dari na fama da rashin samun kudade a wani lokaci cikin shekarar. Wadannan alkaluma ba su nuna rashin jin dadi na dan lokaci ba, amma suna nuna talauci da kuncin rayuwa mai tsanani,” in ji ADC.
A yayin da take mayar da martani kan ikirarin APC game da matakan tattalin arziki, ADC ta ce ‘yan Nijeriya na rayuwa kuncin tattalin arziki, inda farashin man fetur ya karu kusan kashi 500 cikin dari, daga kusan naira 255 a kowanne lita a watan Mayu 2023 lokacin da Tinubu ya hau mulki, zuwa kusan naira 1,500 a kowanne lita a yau a wurare da dama na wannan kasa.
“Wannan yana kara tsadar sufuri kuma yana kara farashi kayayyaki abinci fiye da abin da miliyoyin gidaje za su iya saya.”
ADC ya kara sukar da’awar APC kan kudin da ake kashewa kan tallafin mai, wanda ya kamata ya kai kusan naira tiriliyan 6.4 a asusun ajiya a bara kadai, sai yanzu ne ake karkatar da shi zuwa wasu sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya da ci gaban al’umma.
Jam’iyyar adawa ta ce a rubuce yake cewa naira miliyan 36 kawai, kusan kashi 0.02 cikin dari na manyan ayyuka a cikin kasafin kudin, don ainihin ayyukan jari a shekarar 2025 ga dukkan sashen kula da lafiya na tarayya na Najeriya.
“Saboda haka, ‘yan Nijeriya suna bukatar amsar wadanan tambayoyi masu sauki. Idan an tanadi kudaden tallafin mai tare da rarraba su zuwa muhimman sassan, to a ina dukkan kudin ke tafiya? Me ya sa aka kasa biyan ‘yan kwangiloli na cikin gida? Me ya sa jami’o’i har yanzu ba su da kayan aiki masu kyau?”
[ad_2]
Source link