Dantsoho Ya Karbi Bakuncin Babban Jami’in Ofishin Jakadanacin Daular Larabawa
[ad_1]
Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya karbi bakuncin Babban Jami’i na Ofishin Jakadanacin Daular Larbawa wato UAE, da ke a Nijeriya Salem Al-Jaberi.
Dantsho, ya karbi bakuncinsa ne, a Shalkawar Hukumar NPA, da ke a Marina, a jihar Lagos.
- Cinikayyar Waje Ta Jihar Xinjiang Ta Bunkasa A Shekarar 2025
- Binciken CGTN: Tsarin Diflomasiyyar Amurka Na Babakere Ya Tada Hankula Kan Jagorancin Duniya
Wannnan na daga cikin halartar da Nijeriya ta yi, a wani babban taro, da aka kammala a kwanan baya, a kasar Abu Dhabi, ta ci gaba da kulla alakar fadada bunkasa hada-hadar kasuwanci, a tsakanin kasashen biyu, musamman kan kayana da basu shafi, fannin Man Fetur ba da kara bunkasa fannin Tashoshin Jiragen Ruwa.
Kazalika, ganawar ta su, na zuwa ne, bayan rattaba hannun yarjejeniya a tsakanin Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Teku, Adegboyega Oyetola, da aka yi, a tsakanin Nijeriya, a kasar ta Abu Dhabi.
Bugu ka kari, manufar itace, domin a kirkiro da dabaru ta hanyar yin hadaka domin kara habaka fannin Tashoshin Jiragen Ruwa da safarar kaya, ta hanyar yin amfani da kimiyyar zamani.
A jawabinsa, yayin tattataunawar, Dakta Dantsoho ya bayyana cewa, bisa umarnin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Teku, Adegboyega Oyetola, Hukumar ta NPA, ta himmatu matuka, wajen ganin ana ci gaba da hada karfi da karfe da kasar ta Abu Dhabi, domin kara fadada yawan hada-hadar kasuwanci, musamman a bangare, da bai shafi fannin Mai ba.
“Bisa umarnin umarnin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Teku, Adegboyega Oyetola, muna ci gaba da mayar da hankali, wajen ganin ana ci gaba da hada karfi da karfe da kasar ta Abu Dhabi, domin kara fadada yawan hada-hadar kasuwanci, musamman a bangare, da bai shafi fannin Mai ba, Inji Dantsoho.
A na sa jawabin Babban Jami’i na Ofishin Jakadanacin Daular Larbawa wato UAE Salem Al-Jaberi, kasancewar Nijeriya da kasar ta Abu Dhabi, abokan hadaka ne, ya sanar da cewa, kasar sa, a shirye take, ta kara karfafa hadaka, da Nijeriya.
“Nijeriya da Abu Dhabi, sun jima a matsayin abokan hadaka, a saboda haka, mu a Abu Dhabi, a shirye muke domin mu kara rubanya hadakar hada-hadar kasuwanci, da Nijeriya, ako da yaushe,” A cewarsa.
Ganawar, ta kuma samu halartar Manyan Daraktoci na Hukumar NPA, da suka hada da, Madam Bibian Richard-Edet, da ke a sashen kudi da tafiyarda harkar mulki, sai Injiya Ibrahim Abba Umar, na sahsne kula da kere-kere da Injiya Olalekan Badmus, na sashen gudanawa na Sufurin Jiragen Ruwa a NPA.
Tattaunawar, ta kuma mayar da hankali, kan yadda kasashen biyu, za su amfana da juna, kan bunkasa hada-hadar kasuwanci da samar da damar zuba jari a tsakanin Nijeriya da Daular ta Larabawa.
Kazalika, sun cimma matsayar jadda kara karkafa bunkasa fannin Sufurin Jiragen Ruwa na kasashen biyu da safarar kaya wanda hakan zai sanya, kasashen biyu, su kara bunkasa tatalin arzikinsu.
[ad_2]
Source link