Dalilin Da Ya Sa Sin Ci Gaba Da Zama Babbar Kasuwar Ciniki Ta Duniya
[ad_1]
Gwamnatin Sin ta fitar da wasu alkaluma a jiya Laraba, wadanda ke nuna karuwar cinikayyar shige da fice ta kasar a shekarar 2025, alkaluman sun nuna darajar cinikin waje a bara ta kai Kudin Sin yuan tiriliyan 45.47, wanda ya karu da kashi 3.8 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan. Wannan ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a duniya.
Wannan ba sakamako ne da kasar ta Sin ta samu cikin sauki ba, duba da cewa yanayin tattalin arzikin duniya na yin tafiyar hawainiya, da kuma manufar kariyar cinikayyar kasa da kasa dake kara kunno kai. Nasarar kasar Sin ta samo asali ne daga ingantattun manufofin da kasar ta aiwatar a fannin karfafa gwiwar cinikayyar, kana da kasuwar cikin gida mafi girma, da kuma cikakken tsarin raya masana’antu. Wanda hakan ya zamo ginshigi mai karfi ga shirin ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, tare kuma da kara karfin farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya.
Ci gaban da Sin take samu na bayyana cikin bangarori 3: wato da farko dai, yawan abokan huldar cinikayya ya ci gaba da fadada, inda Sin ke bunkasa cinikayya da kasashe da yankuna sama da 240, daga cikinsu sama da kasashe 190 sun samu karuwar cinikayyar shige da fice.
Na biyu, saurin karuwar kayayyakin fasahar zamani da Sin ke fitarwa ya karu da kashi 11.4 cikin 100, yayin da yawan kayayyaki kamar motoci masu aiki da wutar lantarki da batir ta amfani da hasken rana, da na’urorin samar da wutar lantarki masu aiki da hasken rana da Sin ta fitar ya karu matuka.
Na uku, halin cimma moriya tare ya bayyana a fili. Kamfanonin kasashen waje sun ba da gudummawar kusan kashi 30 cikin 100 na cinikayyar shige da fice, inda shigo da kayayyakin da Sin ta yi ta karu duk da kalubale, kuma ta ci gaba da zama kasuwar shigo da kayayyaki ta biyu mafi girma a duniya. Sin tana ci gaba da more damammakinta tare da sauran sassan duniya ta hanyar bude kofarta.
A daya bangaren kuma, cinikin shige da fice na Sin na bayyana damar samun bunkasuwa ba tare da tangarda ba, da baiwa tattalin arzikin duniya tabbaci da kwarin gwiwa, bisa dogaro da nagartattun manufofin da take dauka, duk da ganin kalubalen da duniya ke fuskanta, yayin da kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ta gyara hasashenta na ci gaban cinikin kayayyaki na duniya har zuwa kashi 0.5 cikin 100 a shekarar nan ta 2026. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link