Douye Diri ya naɗa ɗan uwansa sabon Mataimakin Gwamnan Bayelsa
[ad_1]
Gwamna Douye Diri, ya naɗa wani ɗan uwansa, kuma fasto na cocin RCCG a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa.
Naɗin ya biyo bayan rasuwar tsohon Mataimakin Gwamna, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a ranar 11 ga Disamba, 2025, bayan da ya faɗi a ofishinsa, inda aka yi jana’izarsa a ranar 30 ga Janairu, 2026.
Sabon mataimakin gwamnan, Dokta Peter Pereotubo Akpe, shi ne tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Jihar kafin wannan sabon naɗi.
Haka kuma, shi ne Faston lardi na RCCG mai kula da Province 1 a birnin Yenagoa.
Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ta riga ta amince da naɗin Akpe a matsayin Mataimakin Gwamna.
An bayyana hakan ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata, lokacin da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abraham Ingobere, ya karanta wasiƙar naɗin daga Gwamna Diri.
Lokacin da Akpe ya bayyana a gaban majalisar na ɗan lokaci, an buƙace shi da ya yi gaisuwa ta hanyar sunkuyawa sannan ya fice, kamar yadda dokokin majalisa suka tanada, kasancewar tsohon jagora ne a Majalisar Dokokin Jihar.
Naɗin nasa ya gudana ne bisa tanadin Sashe na 191 (ƙaramin sashe na 3) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), bayan tantancewa da amincewar Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa.
Akpe da Gwamna Diri suna da alaƙa ta jini ta wajen uwa, inda dukkaninsu iyayensu mata suka fito daga al’ummar Ayamasa da ke Ƙaramar Hukumar Ekeremor.
Dokta Akpe wanda ƙwararren malami ne, tsohon ɗan majalisa ne kuma gogaggen ɗan siyasa.
Ya taɓa rike muƙamai da dama a ɓangarorin zartarwa da na majalisa, ciki har da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa da kuma Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gwamna.
Yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanar da Ilimi (Educational Management), kuma yana da ƙwarewa mai zurfi a harkokin mulki, tsara manufofin siyasa da sauye-sauyen ilimi.
Akpe ya fito ne daga Ebedebiri a Ƙaramar Hukumar Sagbama, kuma ya daɗe yana aikin gwamnati a Jihar Bayelsa.
Kafin shigarsa siyasa, ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a gwamnati, ciki har da Shugaban Gudanarwa a Ofishin Mataimakin Gwamna (2006–2007) da kuma Kwamishina a Hukumar Ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa (2008–2011).
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link