Sauya Sheka: Jigo A APC Ya Bukaci Shugabanin Jam’iyyar Su Yi Taka-tsan-tsan
[ad_1]
A jiya ne wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Adamawa, wanda kuma tsohon Sanata ne, Alhaji Abdulrahaman Buba Kwacham ya nemi shugabannin jam’iyyar na kasa su sake nazari tare da taka-tsan-tsan a tsarin nan na bai wa duk wani gwamna da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar matsayin jagoran jam’iyyar a nan take. Ya ce, hakan ba karamar illa zai yi ga tasiri da farin jinin jam’iyyar ba a wurin al’umma talakawa wadanda sune kashin bayan bayan cin dukkan zabukka.
Sanata Kwacham ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ya kara da cewa, wannan wani nau’in zalunci ne kuma yana karya gwiwar ‘yan jam’iyyar da suka tsayu suka bauta wa jam’iyyar da jiki da duniyarsu na tsawon shekaru, sai kawai da rana tsaka wani ya zo ya danne su da sunan ‘Jagoran Jam’iyya’.
- NNPP Ta Yi Watsi DA Rahoton Hukuncin Amurka Kan Kwankwaso
- Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hukumar Alhazai Ta Ƙasa Ambasada Ismail Abba Yusuf
Ya ce, “a halin yanzu muna jin jita-jita cewa, gwamnan mu na jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, ‘tabas muna maraba da shi in ya dawo amma muna kuma bayyana cewa, ba za mu yarda ya kasance jagora a jam’iyyar ba, in kuwa jam’iyyar ta tilasta wa al’ummar Adamawa wannan tsarin to lallai za su yi dana sani”
Ya kuma ce, in har Gwamna Fitinri zai shigo to ya shigo a matsayin dan jam’iyya kamar kowa ba tare da an mika masa ragamar jam’iyyar ba. Domin a kwai wasu da suka yi wa jam’iyya hidima na tsawon shekaru bai kamata a yi watsi da su ba saboda wani gwamna ya shigo ba, in kuma sun ki to za su fuskanci abin da ba sa so a rayuwar jam’iyyar.
Ya kuma bayar da misalin cewa, a wasu jihohi kamar Zamfara da jam’iyyar ta dogara cewa tana da gwamnati amma duk da haka sai da ta rasa kujerar inda Gwamna Dauda Lawal na PDP ya lashe zabe duk da kasancewar suna da Gwamna.
A kan haka ya shawarci shugabannin jam’iyyar APC na kasa da su sake lale in har suna son tabbatar da mulkin APC a jam’iyyar Adamawa.
[ad_2]
Source link